rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu kallo miliyan daya da rabi sun hallara a Rasha

media
Yau ake soma wasannin gasar cin kofin duniya a Rasha. REUTERS/Maxim Shemetov

Yau Alhamis za a fara wasannin gasar cin kofin duniya ta wannan shekara, inda a yau za a fafata wasan farko tsakanin mai masaukin baki Rasha, da kuma Saudiya, a filin wasa na Luzhniki Stadium da ke birnin Moscow.


Gasar da za ta shafe kwanaki 32 tana gudana, za a buga wasanni 64 ne, kamar yadda aka sani a tsakanin kasashe 32.

Ana sa rana masu kallo miliyan daya da rabi ne suka hallara a Rasha domin bai wa idanunsu abinci, yayin wannan gasa, yayin da kuma a gefe guda, jamiā€™ai sukai hasashen cewa sama da masu kallo ta kafar talabijin biliyan uku ne zasu bibiyi wasannin daga inda suke.

Brazil ita ce kasa daya tilo da take samun nasarar halartar kowace gasar cin kofin duniya, ko da yake basu samu nasarar lashe kofin gasar ba tun bayan shekarar 2002.