Hierro ya karbi mukamin horar da 'yan wasan Spain
Tsohon Kaftin din tawagar kwallon kafa ta Spain Fernando Hierro ya karbi rikon kwaryar horar da ‘yan wasan kasar a gasar cin kofin duniya da za a soma wasanninta a yau Alhamis.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hierro ya maye gurbin Julien Lopetegui, wanda hukumar kwallon Spain ta kora a jiya Laraba, kwana guda, bayan da kungiyar Real Madrid ta bayyana shi a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta a kakar wasa mai kamawa.
Hukumar kwallon kafar Spain ta ce ta dauki matakin ne a dalilin rashin sanar da ita a hukumance, dangane da sabon mukamin da Lopetegui ya karba na horar da kungiyar Real Madrid.
Idan za a iya tunawa, a ranar Talata Lopetegui ya sa hannu kan yarjejeniyar horar da ‘yan kungiyar ta Real Madrid tsawon shekaru 3, amma da sharadin zai kama aiki bayan kammala jagorantar ‘yan wasan Spain a wasannin gasar cin kofin duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu