rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Rasha Masar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Salah zai buga wasan da Masar za ta fafata da Rasha

media
Dan wasan gaba na Masar, Mohamed Salah yayin atasaye da abokan wasansa a filin wasa na Ekaterinburg da ke birnin Ekaterinburg na Rasha, kwana guda kafin fafatawar Masar da Uruguay a ranar Juma'a, 15, Yuni, 2018. AFP

Hukumar kwallon kafa ta Masar, ta ce dan wasan kasar Muhd Salah, ya samu isasshiyar lafiyar, buga wasan da Masar din za fafata ranar Talata, tsakaninta da Rasha.


Salah dai bai samu buga wasan farko da Masar ta yi rashin nasara a hannun Uruguay da 0-1 kwallo daya mai ban haushi ba, a ranar Juma'a.

Salah ya samu rauni ne a kafadarsa yayin wasan karshe na 26 ga watan Mayu, da kungiyarsa da fafata da Real Madrid.

Hukumar kwallon kafa ta Masar, ta ce ko a ranar Juma'ar da ta gabata, Salah yana da lafiyar bugawa Masar din wasan da ta yi da Uruguay, kawai dai, mai horar da ‘yan wasan kasar Hector Cuper, ya hutar da shi ne domin bashi damar kara murmurewa.