Isa ga babban shafi
Wasanni

Blatter zai bijirewa takunkumin halartar wasanni da ke kansa

Tsohon shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter na shirin bijirewa takunkunmin haramta mishi shiga ko halartar dukkanin al’muran wasanni da aka kakaba masa, sakamakon samunsa da laifin cin hanci da Rashawa yayin da yake shugabancin hukumar a shekarun baya.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter. AFP
Talla

Wannan yunkuri ya tabbata ne, bayan da wani mai magana da yawun Blatter, ya bayyana cewa tsohon shugaban, na kan hanyar zuwa Rasha a yau Talata, domin halartar kallon wasanni biyu na gasar cin kofin duniya da ke gudana yanzu haka, kana kuma zai gana da shugaban kasar Vladmir Putin.

Sepp Blatter mai shekaru 82, da ya shafe shekaru 17 bisa shugabancin FIFA, ya fuskanci hukuncin haramta mishi shiga dukkan almuran wasanni na tsawon shekaru 6 ne a watan Fabarairu na 2016, bayan da wani kwamitin bincike ya same da laifin biyan wasu kudade dala miliyan 2 ga tsohon shugaban hukumar UEFA Mitchel Platini yayin da suke kan shugabanci, ba bisa ka'ida ba.

Sai dai har yanzu FIFA ba ta ce komai ba, dangane da batun halartar gasar cin kofin duniyar da Sepp Blatter zai yi, inda ake sa ran zai kalli wasan Portugal da Morocco a ranar Laraba, sai kuma wasan Brazil da Costarica a ranar Juma’a, kafin ya koma Switzerland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.