rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Mexico Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

FIFA ta fara bincike kan zargin cin zarafin 'yan wasan Jamus

media
Wasu magoya bayan kasar Mexico, yayin wasan farko na gasar cin kofin duniya ta 2018, na rukuni na 6 da suka fafata da Jamus, a filin wasa na Luzhniki da ke birnin Moscow. Eduardo Verdugo, AP

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce, ta kafa wani kwamitin domin binciken Mexico bayan da wasu magoyan bayan ‘yan wasan kwallon kafa na kasar, suka rika ihun furta wa ‘yan wasan Jamus kalamai na batanci, yayin wasan Mexicon ta samu nasara kan Jamus da kwallo 1-0.


Ko da yake FIFA ba ta yi karin bayani akan takaimaiman yanayi ko irin kalaman cin zarafin da ake zargin magoya bayan Mxico da furtawa ba, sai dai rahotanni sun ce kai tsaye ‘yan Mexicon sun fi mayar da hankali ne wajen cin zarafin mai taron ragar Jamus wato Manuel Neuer.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ko a lokacin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 a Brazil, an samu wasu daga cikin magoya bayan Mexico, da suka rika furtawa abokan hamayyar kasarsu kalaman cin zarafi, sai dai a waccan lokacin FIFA ta kawar da kai.