Isa ga babban shafi
Wasanni

Griezmann ya tsawaita yarjejeniyarsa da Atletico

Dan wasan gaba na Atletico Madrid Antoine Griezmann mai shekaru 27, ya kara wa’adin yarjejeniyar zama da kungiyarsa zuwa shekara ta 2023.

Bafaranshen dan wasan gaba na kungiyar Atletico Madrid Antoine Griezmann.
Bafaranshen dan wasan gaba na kungiyar Atletico Madrid Antoine Griezmann. Federico Gambarini / AFP
Talla

Tsawaita wa’adin yarjejeniyar ya tabbata ne bayan da kungiyar ta Atletico Madrid ta aike da jami’anta, zuwa tawagar kwallon kafa ta Faransa da a yanzu ke Rasha, inda aka daddale.

Mako guda kenan bayan da Griezman ya tabbatar da cewa zai ci gaba da zama a kungiyarsa, duk da cewa mafi akasarin masu bibiyar sha’anin tamaula a duniya, suna da yakinin Griezman zai sauya sheka ne zuwa Barcelona kafin fara sabuwar kakar wasa.

Bayan tsawaita yarjejeniya da Griezman, kungiyar Atletico Madrid ta kuma yi nasarar sayen Thomas Lemar Monaco, wanda shi ma ke takawa kasar tasa Faransa leda a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.