Isa ga babban shafi
Wasanni

Masar da Saudi Arabia sun fice daga gasar cin kofin duniya

Kasashen Masar da Saudi Arabia sun fice daga gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha bayan shan kaye a wasannin zagayen farko da kuma zagaye na biyu da suka ka yi.

Yanzu haka dai kasashen Rasha da Uruguay ne za su dora zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin duniyar.
Yanzu haka dai kasashen Rasha da Uruguay ne za su dora zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin duniyar. Reuters/Henry Romero
Talla

Saudi Arabia ta sha kayen farko a hannun Rasha ne da ci 3 ba ko daya, yayin da ta kara shan kaye hannun Uruguay da ci 1 mai ban haushi.

A bangare guda ita ma Masar ta sha kayen farko a hannun Uruguay da ci daya mai ban haushi yayinda ta yi rashin nasara ta biyu a hannun Rasha da ci 2 da 1.

Wannan dai ne karon farko da Masar din ta halarci gasar cin kofin duniya bayan kusan shekaru 28.

A baya dai akwai kwakkwaran fatan za ta kai wa wani mataki a gasar amma daga bisani al'amura suka sauya ko da dai wasu na alakanta rashin nasararsu ta faro da rashin shigar zakaran kwallon kasar Muhammad Sallah wanda ke fama da jinya.

Sai dai kuma a karawa ta biyu Salah din yayi nasarar zura kwallo guda a ragar Rasha bayanda aka basu bugun Fenalti ko da dai ya gaza farke kwallo na biyun har aka kai ga kammala wasa.

Yanzu haka dai kasashen Rasha da Uruguay daga rukunin A na jadawalin gasar ne za su dora zuwa zagaye na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.