Masar ta fice da gasar cin kofin duniya
Masar ta kama hanyar ficewa daga gasar cin kofin duniya bayan da mai masaukin baki Rasha ta lallasa ta da kwallaye 3-1, a wasan da suka fafata ranar Talata.
Wallafawa ranar:
Kwallon farko da ta shiga ragar Masar dai Kaftin din kasar ne Ahmed Fathy ya zura ta a bisa kuskure, daga bisani kuma Denis Cheryshev da kuma ArtemDzyuba suka zura guda kowannensu, lamarin da ya baiwa Rasha damar kasa ta farko, a gasar cin kofin duniya ta bana da ta fara kaiwa zagayen ragowar kasashe 16.
Masar za ta ci gaba da sa rai ne idan Saudiya ta samu nasara akan Uruguay a wasan da zasu fafata yau Laraba, zalika kuma tilas Uruguay din ta sake yin rashin nasara a wasan karshe na rukuni da za ta yi da mai masaukin baki Rasha, abinda da dama ke da ra’ayin abun da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa.
A bangaren Masar kuwa, kwallo daya tilo da Muhammad Salah ya jefa a bugun daga kai sai mai tsaron gida, ita ce kwallo ta farko da Masar ta ci a gasar cin kofin duniya, tun bayan shekara ta 1990.
Karo na farko kenan da Salah ya bugawa kasarsa wasa, tun bayan raunin da ya samu a kafadarsa, a dalilin ketar dan wasan Real Madrid Sergio Ramos ya yi masa a wasan karshe na gasar zakarun turai ranar 26 a watan Mayu da ya gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu