rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Duniya Rasha Morocco Portugal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Morocco na gab da ficewa daga gasar cin kofin duniya

media
Matukar dai Moroccon ta kara shan kaye a hannun Spain to hakan na nuni da cewa za ta tattara kayanta ta bar Rashan. Pierre René-Worms/RFI

A zagaye na biyu na wasannin gasar cin kofin duniya da ke ci gaba da gudana a Rasha Portugal ta lallasa Morocco da ci daya mai ban haushi a wasan daya gudana yau tsakaninsu wanda shi ne was anta na biyu bayan fara gasar.


Yanzu haka dai wasa daya ya ragewa Moroccon wanda kuma matukar ba ta yi nasara ba za ta tattara yanata-yanata ta bar Rashan.

Tun farko Iran ce ta lallasa Moroccon da ci 1 mai ban haushi a zagayen fark gashi yau kuma Portugal ta kara yi mata makamancinsa.

Kasar da ta ragewa Moroccon ita ce Spain a zagaye na 3 kenan wadda kuma ana ganin abu ne mai wuya ta iya doke ta ganin irin bajintar da ‘yan wasan na Spain suka nuna yayin karawarsu da Portugal a zagaye na farko inda suka tashi ci 3-3.

Sau daya Moroccon ta taba yin gagarumar nasara a kan Portugal a tarihin gasar cin kofin duniyar shi ne a shekarar 1986, inda ta lallasa ta da ci 3 da 1 a zagaye na farko ta kara lallasata a zagaye na biyu yayinda suka yi canjaras a zagaye na 3.

Kuma ita Portugal rabon da wata kasa da ba ta Turai ba ta yi nasara akanta tun a shekarar 2002, inda ko a shekarar 2014 gasar cin kofin duniya da ta gudana kenan, wasa 1 ta yi rashin nasara akansa cikin wasanni 10 da ta fafata a gasar, kuma shi ne wanda Jamus ta doke ta ta kuma lashe kofin na 2014.