rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Duniya Faransa Peru Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta lallasa Peru da ci 1 mai ban haushi

media
Kylian Mbappe bayan zurawa Faransa kwallonta guda a ragar Peru, matakin da ya bata damar tsallakewa zuwa wasannin zagaye na uku. REUTERS/Andrew Couldridge

Faransa ta lallasa Peru da ci 1 mai ban haushi a wasannin zagaye na biyu na cin kofin duniya da ke gudana a Rasha. Matakin dai ya bai wa Faransar damar zama ta biyu a rukuninta na C na jadawalin gasar.


Dan wasan tsakiya na Faransar Kylian Mbappe ne ya zura kwallon a ragar Peru cikin minti na 34 da fara wasa, inda kuma Peru din ta gaza farkewa har zuwa kammala wasan.

Wannan ne dai karon farko da Faransar ta hadu da Peru tun bayan wasan sada zumunta na shekarar 1982 wanda ta lallasa Faransar da ci 1 mai ban haushi.

Dama dai a zagayen farko na gasar cin kofin duniyar Faransa ta lallasa Autralia da 2-1.

Sai dai kafin karkare wasan na yau, alkalin wasa ya bai wa paul Pogba katin gargadi da aka fi sani da Yellow Card.