rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Gasar Cin Kofin Duniya Brazil Costa Rica Rasha Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Brazil ta lallasa Costa Rica da 2 da nema

media
Brazil din dai na da maki hudu yayinda Serbia ke da maki 3. REUTERS/Yves Herman

Brazil ta yi nasarar lallasa Costa Rica da ci 2 da nema a dai dai lokacin da ake gab da karkare wasa. Yanzu haka dai Brazil din ta yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na 3 na gasar cin kofin duniyar da ke ci gaba da gudana a Rasha.


Neymar Junior ne dai ya fara zura kwallon a ragar Costa Rica cikin minti na 90 da fara wasa yayinda Philippe Cautinho ya zura na biyu a minti na 97.

Yanzu haka dai kasashen Brazil da Serbia su ne kan gaba a rukuninsu na E yayinda suka bar kasashen Costa Rica da Switzerland a baya.

Brazil din dai na da maki hudu yayinda Serbia ke da maki 3.