rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gasar duniya: Tun 1938 raban da a fitar da Jamus a matakin rukuni

media
Jamus mai rike da kambin duniya ta gaza tsallakawa matakin gaba a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha REUTERS

A karon farko tun shekarar 1938 kasar Jamus mai rike da kambin duniya ta gaza tsallakawa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya bayan ta sha kasha a hannun Koriya ta Kudu da ci 2-0 a fafatawar da suka yi jiya a Rasha.


Kazalika a karon farko kenan a tarihin Jamus da ta gaza doke wata kasa daga nahiyar Asiya a gasar cin kofin duniya, yayin da a bana ta kammala gasar a can kasan taeburin rukunin F.

Koriya ta Kudu ta jefa kwallaye biyu a mintina na 92 da 96, bayan an kara wa kasashen biyu lokaci bayan kwashe minti 90 ba tare da zura kwallo ko guda ba.

Ko da dai ita ma Koriya ta Kudu za ta tarkata inata-inata zuwa gida, amma ba karamin farin ciki kasar ta yi ba na kafa tarihin fitar da Jamus daga gasar cin kofin duniya.

Kocin Jamus, Joachim Low ya ce, babu shakka wannan cin da aka yi musu zai haifar da cece-kuce mai yawa tsakanin Jamusawa.

Sweden ce ta jagoranci teburin rukunin na F bayan ta casa Mexico da kwallaye 3-0, amma dukkanin kasashen biyu sun tsallaka zagaye na biyu na gasar ta cin kofin duniya.

Ita ma tawagar kwallon kafar Brazil ta tsallaka zuwa matakin gaba na gasar ta cin kofin duniya a Rasha bayan ta samu nasara akan Serbia da kwallaye 2-0.

Yanzu haka Brazil za ta kece raini da Mexico a zagaye na biyu na gasar.

Sai dai a yayin wannan wasa, dan wasan baya na Brazil, Marcelo ya fice daga fili saboda raunin da ya samu.

Da fari dai, dan wasan wanda ke taka leda a Real Madrid ya so ya yi dagiyar ci gaba da wasan amma aka sauya shi da Fillipe Luis.

Ita ma dai Switzerland ta tsallaka zuwa matakin gaba bayan ta tashi 2-2 da Costa Rica, kuma za ta hadu da Sweden a zagayen na gaba.