rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Na dauki alhakin kashin da Najeriya ta sha a Rasha-Ighalo

media
Lokacin da Odion Ighalo ya barar da damar zura kwallo a ragar Argentina a Rasha REUTERS

Dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar Najeriya, Odion Ighalo ya ce, ya dauki alhakin rashin nasarar kasar a wasanta da Argentina a gasar cin kofin duniya a Rasha, in da ya barar da damar zura kwallaye biyu masu kyau a yayin fafatawar wadda ta dauki hankula a sassan duniya.


Ighalo ya nemi afuwan ‘yan Najeriya game da wannan al’amari da ya bakanta ran magoya bayan Super Eagles.

Dan wasan ya ce, lallai wannan rana ta zamo ta bakin ciki a gare shi da ‘yan wasan Super Easgles da daukacin ‘yan Najeriya baki daya.

A bangare guda, Ministan Wasanni da Matasa na Najeriya, Solomon Dalung ya dora laifin ficewar Super Eagles kan dabarun da kocinta Gernot Rohr ya yi amfani da su a yayin fafatawar da Argentina .

Dalung na da ra’ayin cewa, ya kamata ‘yan wasan na Najeriya su rike kwallo a yayin da ya rage minti biyar a tashi wasan, amma hakan ya ci tura har Argentina ta kara kwallao ta biyu a kurarran lokaci.

Shi kuwa gwarzon dan wasan Argentina, Lionel Messi cewa ya yi, lallai Allah ne ya  kwace su a hannun  Najeriya.