Isa ga babban shafi
wasanni

Salah ya tsawaita kwantiraginsa da Liverpool

Dan wasan gaba na Masar da ke taka leda a Liverpool Muhammad Salah ya rattaba hannun kan sabon kwantiragin shekaru 5 da Club din nasa mai doka gasar Firimiya.Sabunta kwantiragin na Salah ya kawo karshen duk wata jita-jitar komawarsa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

A cewar Jurgen Kloop, Liverpool ta yi imani da Salah haka zalika shi ma yana jin dadin kasancewarsa cikinta a don haka babu dalilin tunanin ko dan wasan zai sauya sheka
A cewar Jurgen Kloop, Liverpool ta yi imani da Salah haka zalika shi ma yana jin dadin kasancewarsa cikinta a don haka babu dalilin tunanin ko dan wasan zai sauya sheka REUTERS/Andrew Yates
Talla

Salah mai shekaru 26 wanda ya koma Liverpool daga Roma a waccan kakar kan Yuro miliyan 34 ya zura kwallaye 44 cikin wasanni 52, yanzu sabon kwantiragin nasa wanda zai kai 2023, sai dai sabon kwantiragin bai bayar da wani hurumin yiwuwar katse shi kafin kammaluwarsa ba.

A cewar Jurgen Kloop, Liverpool ta yi imani da Salah haka zalika shi ma yana jin dadin kasancewarsa cikinta a don haka babu dalilin tunanin ko dan wasan zai sauya sheka.

Salah wanda ya yi nasarar lashe takalmin zinare a kakar wasa da ta gabata bayan zama dan wasa mafi zura kwallaye a gasar Firimiya, inda ya zura kwallaye 32 cikin wasanni 38 a gasar Firimiya.

Haka zalika Salah ya yi nasarar zama gwarzon dan wasan shekara a Ingila inda itama kungiyar marubuta wasanni ta karramashi da makamancin mukamin.

A sakonsa bayan kammala sanya hannu kan sabon kwantiragin Salah ya ce yayi farin ciki da ci gaba da kasancewar a Liverpool kuma yana fatan za su kai wani mataki nan gaba kadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.