rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ingila ta tsallake rijiya da baya a gasar kofin duniya

media
Hary Kane na Ingila a yayin fafatawa da Colombia a gasar cin kofin duniya 路透社

Tawagar Kwallon Kafar Ingila ta tsallake rijiya da baya, in da ta samu nasara akan Colombia ta hanyar bugun fanariti a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha, abin da ya ba ta damar kai wa matakin wasan dab da na kusa da na karshe, wato kwata fainal a gasar.


Kasashen biyu sun buga fanaritin ne bayan shafe tsawon minti 90 har ma da kari suna kan kunnen doki 1-1, yayin da Eric Dier ya zura kwallon da ta bai wa Ingila nasara bayan Carlos Bacca na Colombia ya barar da fanaritinsa.

A karon farko kenan a tarihi da Ingila ke samun nasara ta hanyar bugun fanariti a gasar cin kofin duniya, yayin da za ta hadu da Sweden a matakin wasan dab da na kusa da na karshe.

Ita ma Sweden ta samu nasarar kai wa wannan matakin ne bayan ta yi wa Switzerland ci 1 mai ban haushi.

A ranar Jumma’a mai zuwa ne za a fara fafatawa a matakin kwata fainal na gasar ta cin kofin duniya, in da Uruguay za ta hadu da Faransa, sai kuma Brazil da za ta kece raini da Belgium.