rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Zan horar da 'yan wasan Argentina a kyauta- Maradona

media
Diego Maradona ya yi fatan ina ma Allah ya ba shi karfin bugawa kasarsa kwallon kafa kamar yadda ya yi a can baya REUTERS/Charles Platiau

Tsohon gwarzon dan kwallon kafar Argentina, Diego Maradona ya nemi kasar da ta ba shi damar horar da ‘yan wasanta a kyauta, bayan Faransa ta yi waje da kasar a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha.


Hukumar Kwallon Kafar Kasar na fatan murabus din kocinta na yanzu, Jorge Sampaoli bayan ya gaza kai kasar ga gaci a gasar ta bana.

Sai dai Sampaoli ya hakikance cewa, zai ci gaba da jagorantar tawagar, kuma muddin aka kore shi daga wannan kujera, to ana ganin zai bukaci kasar da ta biya shi dukkanin albashinsa na kwantiragin shekaru hudu da ya kulla da ita, kuma kudaden za su kai Pam miliyan 16.8.

Ana ganin cewa, Hukumar Kwallon Kafar na kyashin biyan shi wadannan makudaden kudade musamman a dai dai wannan lokaci da take fama da matsalar kudade.

Maradona wanda ya jagoranci Argentina wajen lashe kofin duniya a shekarar 1986, ya ce, a shirye yake ya koma aikin horar da 'yan wasan kasar ba tare da biyan shi ko sisi ba.

"Abin takaici ne yadda Faransa ta fitar da kasata daga gasar cin kofin duniya  bayan ma Faransan ba ta cikin daya daga cikin zaratan kasashe a gasar ta bana" In ji Maradona.

Tsohon dan wasan ya ce, ya na matukar bakin cikin ganin doke kasarsa a gasar, in da ya yi burin ina ma Allah ya ba shi karfin bugawa kasar tamaula.