Isa ga babban shafi
Wasanni

Real Madrid ta musanta yunkurin sayen Mbappe daga PSG

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta musanta rahotannin da cewa ta amince za ta sayi dan wasan gaba na kasar faransa da ke taka leda a kungiyar PSG Kylian Mbappe.

Dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappé yayin murnar zura kwallo a ragar Argentina yayin wasan da Faransa ta samu nasara da 4-3 a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha.
Dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappé yayin murnar zura kwallo a ragar Argentina yayin wasan da Faransa ta samu nasara da 4-3 a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha. REUTERS/Michael Dalde
Talla

A ranar 4 ga watan Yuli na shekarar 2018, jaridar labaran wasanni ta AS da ke kasar Spain ta rawaito cewa, Madrid ta cimma yarjejeniya da takwarar ta ta PSG wajen sauyin shekar Mbappe mai shekaru 19 kan kudi fam miliyan 240.

Karo na biyu kenan Real Madrid tana musanta rahoton ta sayi sabon dan wasa, bayan da a ranar Litinin da ta gabata, ta karyata rahoton da aka dade ana yadawa, na cewa ta neman sayan dan wasan gaba na kungiyar ta PSG Neymar idanu a rufe.

A watan Agustan shekarar da ta gabata Mbappe ya koma kungiyar PSG daga Monaco a matsayin aro kan kudi euro miliyan 166, ranar 1 ga watan Yulin wannan shekarar kuma, kungiyar ta PSG ta tabbatar da kammala sayen dan wasan daga Monaco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.