rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta fitar da Uruguay daga gasar cin kofin duniya

media
Dan wasan Faransa Raphaƫl Varane yayin murnar zura kwallon farko a ragar Uruguay, a wasan zagayen gaf da na kusa da karshe da Faransar ta lallasa Uruguay da kwallaye 2-0. REUTERS/Damir Sagolj

Kwallayen da Varane hadi da Griezman suka jefa a ragar Uruguay sun bai wa Faransa nasarar samun kai wa ga zagayen wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha.


Karo na farko kenan da Faransa ta samu nasara wajen kai wa matakin kusa da na karshe a gasar ta cin kofin duniya tun bayan shekarar 2006.

A nata bangaren kuwa, wannan rashin nasara da kasar Uruguay ta yi, ita ce ta farko da ta fuskanta, a dukkanin wasannin da ta buga na gasar cin kofin duniya ta bana da Rasha ke karbar bakunci.

A halin yanzu Faransa za ta yi dakon wanda zai yi nasara a tsakanin Brazil da Belgium, domin fafatawa da shi a zagayen kusa da na karshe a filin wasa da ke birnin Saint Petersburg ranar Talata mai zuwa.