rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Harry Kane ka iya lashe kyautar yawan zura kwallaye a Rasha

media
Dan wasan gaba na Ingila Harry Kane yayin murnar zura kwallo ta biyu da ya jefa a ragar Tunisia. REUTERS/Sergio Perez

Dan wasan gaba na kwallon kafar Ingila, Harry Kane na ci gaba da jagorantar fafutukar lashe kyautar dan wasan da ya fi yawan zura kwallaye a gasar cin kofin duniya ta bana da ke gudana a Rasha.


Idan har burin Harry Kane ya tabbata, zai zama dan wasan Ingila na farko da ya samu wannan kyauta, bayan makamancin tarihin da dan wasan kasar ta Ingila Gary Lineker ya kafa shekaru shekaru 32 da suka gabata.

A gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986 ne Lineker ya ci wa Ingila kwallaye shida a wasannin da ya buga mata, abinda ya bashi damar lashe kyautar dan wasa mafi yawan kwallaye a gasar.

Yayinda da gasar cin kofin duniya ta bana ke gudana a yanzu aka, Harry Kane yana da kwallaye 6, wadanda ya samu zurawa a wasannin da Ingila da buga da kasashen Tunisia, Panama da kuma Colombia.