rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sama da mutane 280,000 na korafi kan wasan Ingila da Colombia

media
Wasu daga cikin 'yan wasan Colombia yayin da takaddama da barke tsakaninsu da na Ingila, a lokacin da suke fafatawa a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha. REUTERS

Sama da masu kallon wasanni dubu 280, sun rattaba hannu kan amincewa da wata takardar korafi da ke neman hukumar FIFA, ta bada umarnin sake haska bidiyon wasan da aka yi tsakanin Ingila da Colombia a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya.


Wadanda suka rubuta takardar korafin sun ce akwai kurakurai da dama da alkalan wasa suka tafka yayin fafatawar tsakanin Ingila da Colombia, daya daga ciki kuma shi ne damar bugun daga kai sai mai tsaron raga da Alkalin wasa ya baiwa Ingila wanda ya bai wa Harry Kane damar jefa musu kwallo.

Yayin fafatawar da suka yi alkalin wasa dan kasar Amurka Mark Giergia ya busawa Colombia aikata laifuka 23, yayin da Ingila ta aikata laifuka 13, zalika 6 daga cikin katunan gargadi na dorawa da alkalin wasan ya nuna, ya bai wa ‘yan wasan Colombia ne, yayin da na Ingila suka samu guda biyu, wasu daga cikin dalilan da suka sa kenan, dubban daruruwan masu korafi ke neman FIFA ta sake duba sakamakon wannan wasa.