rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Croatia ta fitar da Rasha daga gasar cin kofin duniya

media
Yan wasan Croatia yayin murnar samun nasarar kai wa zagayen kusa da na karshe. REUTERS/Henry Romero

Kasar Croatia ta samu nasarar kai wa zagayen kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya, bayan doke mai masaukin baki Rasha da kwallaye 4-3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.


Da farko dai an tashi kunnen doki ne (1-1), bayan shafe mintuna 90 ana fafatawa tsakanin kasashen, sai dai daga bisani bayan shiga wasu mintuna dukkanin kasashen biyu suka sake samun nasarar jefa karin kwallaye a ragar junansu inda aka kammala mintunan karin lokaci wasa 2-2, hakan ta sa tilas a kai ga matakin bugun daga kai sai mai tsaron gida.

A halin yanzu Croatia za ta fafata ne da kasar Ingila wadda ta samu nasarar kai wa zagayen kusa da na karshen gasar cin kofin duniyar, bayan lallasa kasar Seweden da kwallaye 2-0.

‘Yan wasan Ingila Dele Alli da Harry Maguire ne suka ci kwallayen da suka bai wa kasar damar zuwa matakin zagayen wasan kusa da na karshe, a karon farko cikin shekaru 28.