rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta samu zuwa wasan karshe a Rasha bayan lallasa Belgium

media
Rabon Faransa da kai wa wannan mataki dai tun a zamanin su Zidane, yayin gasar cin kofin duniya da ta gudana a Jamus a shekarar 2006. REUTERS/Lee Smith

A wasan gab dana karshe na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha, Faransa ta lallasa Belgium da ci daya da Nema, matakin da ya bata damar tsallakawa zuwa zagayen wasan karshe wanda za ta kara ko dai da Croatia ko kuma da Ingila a ranar Lahadi mai zuwa.


Dan wasan Faransar Samuel Umtiti ne ya zura kwallon a minti na 51 da fara wasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Wasan na yau dai ya gudana ne a gaban idon shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron wanda ya halarci filin wasan.

Kamar dai yadda aka yi hasashe hakan ne ya faru domin kuwa Belgium ba ta taba yin nasara kan Faransa ba a tarihin kwallon kafa musamman a babban wasa.

Bayan nasarar ta yau, ya zama kenan sau uku a tarihi Faransar na lallasa Belgium a gasar cin kofin duniya lokaci daban-daban.

Rabon Faransa da kai wa wannan mataki dai tun a zamanin su Zidane, yayin gasar cin kofin duniya da ta gudana a Jamus a shekarar 2006.