rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Croatia ta tsallaka wasan karshe a gasar kofin duniya

media
Luka Modric da Dejan Lovren na Croatia na murnar samun nasara REUTERS/Kai Pfaffenbach

Kasar Croatia ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha bayan ta doke Ingila da kwallaye 2-1.


Yanzu haka Croatia wadda a karon farko kenan da take samun gurbi a wannan mataki, za ta kece raini da Faransa a wasan karshe a ranar Lahadi.

Kasashen biyu sun fara shafe tsawon mintina 90 suna kan kunnen doki 1-1, lamarin da ya sa aka kara musu lokaci, yayin da Croatia ta kara kwallo ta biyu ta hannun Mario Mandzukic.

Ingila ce ta fara zura kwallo a minti na 5 da saka wasan ta hannun Kieran Trippier, amma Ivan Perisic ya farke a minti na 68.

Tarihi ya nuna cewa, a can baya, kasashen biyu sun hadu sau daya a wata babbar gasa, in da Ingila ta samu nasara da ci 4-2 a matakin rukuni a shekarar 2004 a gasar cin kofin kasashen Turai.

Amma a jumulce, sun hadu sau takwas, in da Ingila ta samu nasara a wasanni hudu ,Croatia ta samu nasara a wasanni uku, sannan suka tashi canjarasa a wasa guda.