rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nadal zai fafata da Djokovic karo na 52 a gasar Wimbledon

media
Rafeal Nadal, yayin da yake murnar samun nasara akan Juan Martin Del Potro a zagayen gaf da na kusa da karshe na gasar Wimbledon da ke gudana a London.. AFP/Glyn KIRK

Gwarzon dan wasan Tennis lamba daya na duniya Rafeal Nadal dan Spain zai fafata da abokin hamayyarsa Novak Djokovic na kasar Serbia, a zagayen kusa da na karshe na gasar Wimbledon da ke gudana a London.


Karo na shidda kenan da Nadal ya samu kai wa zagayen kusa da na karshen a gasar tennis ta Wimbledon, bayan da a wasan kwata Final na jiya Laraba, Nadal din ya samu nasara kan Juan Martin Del Potro na Argentina da kwallaye 7-5, 6-7, 4-6, 6-4 da kuma 6-4.

Sai da aka shafe sa’o’i 4 Nadal da Del Potro suna fafatawa kafin Nadal ya samu nasarar da kyar.

Sau 51 aka taba haduwa a wasan na tennis tsakanin Djokovic da Nadal, inda Nadal ya samu nasara sau 25, Djokovic kuma ya samu nasara akan Nadal sau 26.