rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Serena za ta fafata da Kerber a Wimbledon

media
Serena Williams RFI/Pierre René-Worms

Gwarzuwar ‘yar wasan kwallon Tennis, Serena Williams za ta kara da Angelique Kerber ta Jamus a gasar Wimbledon ta mutum dai-dai bayan zaratan biyu un tsallaka zuwa matakin wasan karshe na wannan gasa.


Williams Ba’amurikiya da ta kasance lamba ta daya a duniyar kwallon tennis a can baya, ta casa Julia Gorges ta Jamus da ci 6-2 da 6-4, yayin da Kerber ta casa Jelena Ostapenko ta Latvia da ci 6-3 da kuma 6-3.

A ranar Asabar mai zuwa ne zaratan biyu za su kece raini da juna, wasan da ake kallo tamkar maimaicin fafatawar da suka yi da juna a irin wannan mataki a shekarar 2016, in da Serena Williams ta yi nasara.

A karo na 24 kenan da Williams ke neman lashe kambi a manya-manyan gasar Tennis wato Grand Slam, amma a karon farko kenan tun bayan da ta haihu a cikin watan Satumban bara.