Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya goyi bayan shawarar sayar da Dembele - Rahoto

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi ya bukaci kungiyar da ta sayar da sabon dan wasan da ta sayo daga kungiyar Dortmund, Ousmane Dembele, domin ta sayi dan wasan Chelsea Eden Hazard.

Lionel Messi.
Lionel Messi. Reuters/Albert Gea
Talla

Mujallar wasanni ta ‘Don Balon’ da ake wallafa ta Spain, ta rawaito Messi yana bayyana ra’ayin na sa ne kan sayen Hazard, yayin da yake hutu a a tsibirin Ibiza da ke Spain.

Mujallar ta Don Balon ta kuma rawaito cewar mafi akasarin ‘yan wasan Barcelona na goyon bayan shawarar sayar da Dembele, domin maye gurbinsa da Eden Hazard.

Kafin wannan lokacin dai wasu kafafen yada labarai a Spain sun rawaito cewa kungiyar Barcelona ta fara kokarin sayen Hazard daga Chelsea, baya ga William da take neman sayo shi daga kungiyar ta Chelsea, kimanin watanni uku da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.