Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta gaza kare kambinta a gasar kokowar damtse

Najeriya ta kare a mataki na biyu a gasar kokowar hannu ko ta damtse ta nahiyar Afrika, kashi ta 9 da aka kammala jiya lahadi a kasar Ghana.

Wasu 'yan wasan kokowar kwanji a nahiyar Afrika.
Wasu 'yan wasan kokowar kwanji a nahiyar Afrika. The Guardian Nigeria
Talla

Kasar Ghana mai masaukin baki ce ta lashe gasar bayan samun nasarar cin lambobin yabo na Zinare 31, Azurfa 32 da kuma Tagulla 25, inda ta samu maki 777.

Najeriya da ke a matsayi na biyu, ta lashe kyautar Zinare 6, Azurfa 6, da kuma Tagulla 6, inda ta samu maki 112.

Kasar Mali ce ta kammala gasar a matsayi na uku, bayan lashe kyautar Zinare 6, da kuma Azurfa 4.

Sauran kasashen da suka fafata a gasar kokowar ta Damtse sun hada da Masar wadda ta samu labobin yabo 4, Togo mai lambobin yabo 6, sai kuma Kamaru da ta lashe kyautar lambobin yabo 2.

A shekarar bara dai Najeriya ce ta zama zakara a wannan gasa, wadda ta karbi bakuncinta a birnin Legas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.