rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Duniya Jamus Najeriya Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jamus ta doke Najeriya a wasan farko na gasar cin kofin duniya

media
'Yan wasan Najeriya na Falconets, yayin fafatawa da takwarorinsu na Jamus. Richard Wolowicz/Getty Images

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta mata ta Falconets, ta yi rashin nasara a wasan farko da ta fafata tsakaninta da Jamus a gasar ci kofin duniya na mata na ‘yan kasa da shekaru 20, da Faransa ke karbar bakunci.


Jamus ta samu nasara kan Najeriya da 1-0 (ci daya mai ban haushi) ne ta hannun ‘yar wasanta Stefanie Saunders a wasan da suka fafata a yau litinin 6 ga watan Agusta, 2018.

Kasashen da Najeriya za ta fafata da su a wasannin gaba na matakin rukuni, sun hada da China da kuma Haiti.

A sauran wasannin da aka fafata a yau Litinin, China ta samu nasara kan Haiti da kwallaye 2-1, sai kuma Spain da ta lallasa Paraguay da kwallaye 4-1.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi na farko a ranar Lahadi, sun hada da fafatawa tsakanin Faransa da Ghana, inda ‘yanmatan Faransar suka casa na Ghana da kwallaye 4-1.

Holland kuwa ta samu nasara kan New Zealand da kwallaye 2-1.

Gasar wadda aka soma ta a ranar lahadi 5 ga watan Agusta za ta kare a ranar 24 ga watan.