Isa ga babban shafi
Wasanni

"Manchester United na fuskantar kaka mai wahala"

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Jose Mourinho ya ce, kungiyar na fuskantar kakar wasanni mai wahala, har sai ta karfafa tawagarta gabanin rufe kasuwar cefanen ‘yan wasa nan da ranar Alhamis mai zuwa.

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho.
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho. Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Wannan na zuwa ne bayan Manchester United ta kammala wasan share fagen shiga kaka da ci daya mai ban haushi da ta sha a hannun Bayern Munich ta Jamus, kuma Javi Martinez ne ya zura kwallon daya tilo a wasan na ranar Lahadi.

Mourinho ya ce, shugaban kungiyar ta Manchester United ya san abin da yake so kuma kwanaki kalilan suka rage masa don ganin abin da zai faru.

Mourinho ya bada misali da Liverpool da ya ce, tana lale kudade don siyan komai da koma da zimmar karfafa kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.