rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An rufe kasuwar musayar 'yan wasa a Ingila

media
Kungiyoyin Kwallon Kafa na Ingila na da damar kulla kwantiragi da 'yan wasa akan aro har nan da karshen watan Agusta REUTERS/Nigel Roddis

An rufe kasuwar musayar ‘yan wasa kwallon kafa a Ingila amma kungiyoyin da ke buga gasar firimiyar kasar na da damar ci gaba da kulla kwantiragi da ‘yan wasa akan aro har nan da karshen watan Agusta.


A ranar 31 ga watan na Agusta ne za a rufe kasuwar musayar a Scotland da kusan daukacin manyan kasashen Turai da ke shirya gasar lig-lig.

Daya daga cikin manyan abubuwan da suka dauki a hankali a yayin musyar ‘yan wasan a Ingila, shi ne yadda kocin Manchester United, Jose Mourinho ya koka kan rashin sayen karin sabbin ‘yan wasa don karfafa tawagarsa.

A yayin wani taron manema labarai, Mourinho ya ce, ba shi da kwarin gwiwa game da sayen karin sabbin ’yan wasan, don haka dole ne ya mayar da hankali kan ‘yan wasan da yake da su.

Kawo yanzu Manchester United ta kulla kwantiraghi da ‘yan wasa uku a wannan kaka da suka hada da Fred na Brazil da Diogo Dalot na Portugal da kuma Lee Grant mai tsaren raga, amma duk da haka Mourinho na matukar burin kara karfafa tawagarsa musamman ganin yadda suka kare a mataki na biyu a teburin gasar firimiya ta kakar da ta gabata, in da Manchester City ta ba ta tazamar maki 19.

A bangare guda rahotanni na cewa, kungiyar Arsenal ta gabatar da zunzurutun Pam miliyan 92 don saye dan wasan gaba na Barcelona Ousmane Dembele kamar yadda wani dan jarida daga Spain Kike Marin ya bayyana.

Mr. Marin ya bayyana haka ne a wannan yammaci a shafinsa na Twitter, amma ya ce, akwai yiwuwar Arsenal ta janye yarjejeniyar don watakila Dembele ya amince ko kuma akasin haka kamar yadda ya ce.

Ita ma West Ham ta kulla kwantiragin shekaru uku da Lucas Perez daga Arsenal, yayin da Everton ta kammala kulla kwantiragi da Yerry Mina daga Barcelona.