rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kammala cin kasuwar musayar 'yan wasa ta Ingila

media
Wannan ne karon farko da kungiyoyin kwallon kafar suka bi doka wajen kammala sayen 'yan wasan akan ka'ida. REUTERS/Nigel Roddis

An kammala kulle kasuwar cinikayyar ‘yan wasa yau a Ingila gabanin fara doka wasannin gasar Firimiya, kuma wannan ne karon farko da aka tabbatar da dokar wajen kulle kasuwar kafin fara wasa.


An karkare cinikayyar ‘yan wasan a bangaren Firimiyar Ingilan da cinikin mai tsaron raga mafi tsada a tarihi Kepa Arrizabalaga wanda Chelsea ta sayo daga Atletic Bilbao kan Yuro miliyan 80 bayan sallamar da mai tsaron ragarta ga Real Madrid.

Kididdiga dai ta nuna cewa anyi cinikin akalla ‘yan wasa 122 a kan kudi yuro biliyan 1 da miliyan 26, inda a wannan karon masu tsaron raga biyu ke kan gaba a matsayin mafiya tsada a kasuwar musayar ‘yan wasan ta Ingila wato Kepa kan yuro miliyan 88 da Alisson kan yuro miliyan 66 sai kuma Riyad Mahrez kan yuro miliyan 60.

Kungiyoyi irinsu Manchester United Tottenham sun gaza sayen ‘yan wasan da suke muradi musamman United da ke neman karin dan wasan baya.