Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo ya ci wa Juventus kwallon farko a wasan sada zumunci

Cristiano Ronaldo ya ci wa Juventus kwallon farko a wasan da ya fara buga mata na sada zumunci, wanda suka fafata da karamar tawagar kungiyar tasu.

Wani magoyin bayan Critiano Ronaldo yayin kokarin daukar hoto da dan wasan, yayin da suke fafata wasan sada zumunci a filin wasa na Villar Perosa da ke birnin Turin, a kasar Italiya, 12 Agusta, 2018.
Wani magoyin bayan Critiano Ronaldo yayin kokarin daukar hoto da dan wasan, yayin da suke fafata wasan sada zumunci a filin wasa na Villar Perosa da ke birnin Turin, a kasar Italiya, 12 Agusta, 2018. REUTERS/Massimo Pinca
Talla

Wasan sada zumuncin, wanda aka soma tun a shekarar 1955, an saba buga shi a duk shekara a tsakanin tawagar kwararrun kungiyar ta Juventus ta A, da kuma tawaga ta biyu ta B, kuma wasan yana gudana ne a garin Villar Perosa da ke wajen birnin Turin.

‘Yan kallo dai sun yi ta ambaton sunan Ronaldo tare da bayyana fatan zuwansa Juventus zai taimaka wa kungiyar, wajen lashe kofin gasar zakarun nahiyar Turai.

Da dama daga cikin magoya bayan kungiyar ta Juventus, sun sanya riguna masu dauke da sunan Ronaldo da lamba bakwai, lamarin da ke nuna kyakkyawan fata da suke na sa ran lashe kofin zakarun Turai a kakar wasa ta bana.

A karshen wasan sada zummuncin dai tawagar farko ta kungiyar Juventus, wato su Ronaldo sun lallasa tawagar kungiyar ta biyu da kwallaye 5-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.