Isa ga babban shafi
Wasanni-Zakarun Turai

Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta mika kyautar gwarzon dan wasan shekara na nahiyar ga Luka Modric dan wasan kasar Crotia da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid yau a Monaco bayan rawar da ya taka a kakar wasan da ta gabata.

Modric mai shekaru 32 ya ce ya yi matukar alfahari da lambar yabon tare da mika godiya ga ilahirin wadanda suka horar da shi tamaula a gida da kuma a bangaren kungiyoyi.
Modric mai shekaru 32 ya ce ya yi matukar alfahari da lambar yabon tare da mika godiya ga ilahirin wadanda suka horar da shi tamaula a gida da kuma a bangaren kungiyoyi. REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Bayan karbar lambar yabon Modric, ya yaba da irin dawainiyar da ya ce mahaifinsa ya yi masa wanda shi ne ya jajirce tare da bashi kwarin gwiwar ganin ya kai matsayin da ya ke yanzu.

Modric wanda ya tallafawa Club dinsa wajen lashe kofin zakarun Turai karo na 3 a jere ya kuma yi rawar gani a gasar cin kofin duniya inda ya kusa kai kasar ta sag a nasarar lashe kofin duniya kafin faransa ta yi waje da su.

Modric mai shekaru 32 ya ce ya yi matukar alfahari da lambar yabon tare da mika godiya ga ilahirin wadanda suka horar da shi tamaula a gida da kuma a bangaren kungiyoyi.

Luka wanda ya faro kwallonshi da Club din Dinamo Zagreb kafin kulla kwantiragin shekaru 4 da Tottenham daga bisani kuma Real Madrid ta saye shi kusan shekaru 6 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.