Isa ga babban shafi
Wasanni-Zakarun Turai

UEFA ta fitar da jadawalin gasar zakarun Turai na bana

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta fitar da jadawalin kungiyoyi 32 da za su fafata a gasar lashe kofin zakarun Turai, inda ta rarraba su zuwa rukuni 8.

Jadawalin ya nuna cewa Ronaldo zai kara da Manchester United yayinda Neymar Junior da Muhammad Salah za su hadu da juna.
Jadawalin ya nuna cewa Ronaldo zai kara da Manchester United yayinda Neymar Junior da Muhammad Salah za su hadu da juna. REUTERS/Jean Pierre Amet
Talla

Rukunin farko na jadawalin, wato rukuni A ya kunshi kungiyoyi irinsu Atletico Madrid da Dortmund da Monaco da Club Brugge.

Sai kuma rukunin B da ya kunshi Barcelona da TOTTENHAM da PSV da kuma Inter Milan.

Akwai kuma rukunin C da ya kunshi PSG da Napoli da LIVERPOOL da kuma Red Star Belgrade.

Yayinda rukunin D ya kunshi kungiyoyi irinsu Lokomotiv Moscow da Porto da Schalke da kuma Galatasararay.

Akwai kuma rukunin E daya kunshi Bayern Munich da Benfica da Ajax da kuma AEK Athens.

Ka zalika rukunin F ya kunshi kungiyoyi irinsu MAN CITY da Shakhtar da Lyon da kuma Hoffenheim.

Rukunin G kuma akwai mai rike da kambu Real Madrid da Roma da CSKA Moscow da Viktoria Plzen.

Yayinda rukunin H kuma ya kunshi Juventus da MAN UTD da Valencia da kuma Young Boys.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.