rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Seychelles Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Super Eagles ta lallasa Seychelles har gida da ci 3 da nema

media
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles. Reuters/Peter Cziborra

Super Eagles ta Najeriya ta yi nasarar lallasa Pirate ta Seychelles da ci 3 da nema a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika da za ta gudana a Kamaru cikin shekarar 2019.


Super Eagles din ta samu kwallayenta uku ne daga Ahmed Musa da Chidozie Awaziem da kuma Odion Oghalo.

Wasan dai shi ne karon farko a tarihin tamaula da kasashen biyu suka kara da juna.

Seychelles ba ta taba samun gurbin fafatawa a gasar ta cin kofin Afrika ba, yayinda Najeriya kuma rabonta da zuwa gasar tun a shekarar 2013 bayan lashe kofin.

A bangaren guda itama Kenya ta lallasa Ghana da ci daya mai ban haushi, sai kuma Namibia da itama ta lallasa Zambia da ci da ya da nema duk dai a wasannin na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika.