Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ka iya haramtawa Saliyo shiga wasanni

Kasar Saliyo na fuskantar hadarin cin karo da fushin hukumar kwallo kafa ta duniya FIFA, wadda ka iya haramta mata shiga wasanni.

Wani sashi na harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a birnin Zurich, na kasar Switzerland.
Wani sashi na harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA a birnin Zurich, na kasar Switzerland. REUTERS/Arnd Wiegmann/Files
Talla

Lamarin ya biyo bayan, samamen da jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa na kasar ta Saliyo suka kai kan ma'aikatar hukumar wasannin kasar a jiya Talata, inda suka samu shaidu kan zargin da ake yiwa shugabancin hukumar na cin hanci da rasahawa.

Tun a makon da ya gabata, hukumar yakar cin hanci da rashawar ta Saliyo, ta aikawa shugabar hukumar kwallon kafar Isha Johansen wasika, inda ta umurce ta da ta sauka daga mukaminta, sakamakon zarginta da laifin bayarwa ko karbar na goro, dangane da shirya sakamakon wani wasan neman cancantar halartar gasar cin kofin duniya da tawagar kwallon kafar kasar ta fafata a baya.

Tuni dai aka haramtawa Johansen da kuma sakatarenta Chris Kamara, shiga ginin hukumar kwallon kafar kasar ta Saliyo, duk da cewa sun musanta zargin da ake musu.

A farkon makon da muke ciki hukumar FIFA ta ce tana bibiyar abinda ke faruwa a Saliyo, ta kaddamar da nata binciken, kan zargin da ake yiwa Isha Johansen wajen kokarin sayen wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya, da Saliyo ta fafata da Afrika ta Kudu a shekarar 2008.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.