Isa ga babban shafi
Wasanni

Zargin da ake yiwa Ronaldo yana damun mu - Nike

Kamfanin Nike dake Amurka, da ya shahara wajen sana’anta kayayyakin wasanni ya ce, ya damu matuka, dangane da zargin cin zarafi ta hanyar aikata fyade, da ake yiwa dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo.

Tsohon dan wasan Real Madrid da ya koma Juventus, Cristiano Ronaldo.
Tsohon dan wasan Real Madrid da ya koma Juventus, Cristiano Ronaldo. Heino Kalis/Reuters
Talla

Nike, wanda ya kulla yarjejeniyar dala biliyan 1 da Ronaldo ta ban gishiri in baka manda, ya ce zai ci gaba da bibiyar yadda lamarin zargin da ake yiwa dan wasan ke warwara, domin tantance makomar yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

A gefe guda, kamfanin EA Sports da shima ya shahara wajen sana’anta na’urorin wasannin bidiyo musamman na kwallon kafa, wanda shi ma ke da yarjejeniya da Ronaldo, ya ce ya soma nazarin makomar alakar da ke tsakaninsu.

Tun a ranar Larabar da ta gabata, Cristiano Ronaldo ya sake musanta zargin da Kathryn Mayorga ta yi masa, na cin zarafinta ta hanyar fyade, a wani Otal din Las Vegas dake Amurka a shekarar 2009.

Akwai fargabar cewa lamarin ka’iya shafar yarjejeniyoyin da Ronaldo ya kulla da kamfanonin, abinda ka ‘iya haifar masa da nakasu wajen makudan kudaden da yake samu.

Sai dai kungiyar dan wasan wato Juventus ta ce

zargin da Kathryn Mayorga ke yiwa dan wasanta Cristiano Ronaldo ba zai shafi kyakkyawar alakar dake tsakaninsu.

Juventus ta ce ta gamsu da irin gudunmawar sabon dan wasan nata, da kuma irin kishin da yake nunawa cigabanta, dan haka shugabanni da magoya bayanta suna bayan Ronaldo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.