Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta soke wasan Ghana da Saliyo

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta soke wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika da za a yi tsakanin Ghana da Saliyo, a Alhamis dinnan a garin Kumasi.

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino. Reuters
Talla

Soke wasan ya biyo bayan matakin da FIFA ta dauka na kin amincewa da bukatar gwamnatin Saliyo, kan neman dagewa kasar haramcin buga wasanni da ta kakaba mata a dalilin katsalandan da hukumar ta FIFA ta ce gwamnatin kasar tayi cikin al’amuran hukumar wasannin kasar.

A makon da ya gabata FIFA ta haramtawa Saliyo shiga wasanni, bayanda hukumar yakar cin hanci da rashawa ta kasar, ta sanar da tsige Isha Johensen shugabar hukumar kwallon kafar kasar, da kuma sakatarenta Christopher Kamara, bisa zarginsu da cin hanci da rashawa, wajen tsarawa kasar wasannin da zata buga.

Kafin matakin soke wasan dai, FIFA ta gindaya Saliyo sharadin tilas a mayar da Isha Johensen da kuma sakatarenta kan mukamansu, kafin dagewa kasar haramcin wasanni, sai dai Mazzola Kamara, wanda ya maye gurbin tsohuwar shugabar kwallon kafar kasar, ya tabbatar da cewa, sharadi ne da gwamnati ba za ta amince da shi ba.

A bangaren hukumar kwallon kafar nahiyar Afrika CAF kuwa, har yanzu, ana dakon ganin matakin da za ta dauka, dangane da ka’idar baiwa Ghana maki 3, a matsayin wadda ta samu nasara kan Saliyo a wasan na ranar Alhamis da bai yiwu ba, kamar yadda ka’idar wasanni ta tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.