Isa ga babban shafi
Wasanni

Mai horar da 'yan wasan Libya yayi murabus

Mai horar da tawagar kwallon kafa na Libya Adel Amrouche ya ajiye aikinsa, yayinda ya rage lokaci kalilan kasar ta fafata wasan neman tikitin zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika da Najeriya a garin Uyo dake jihar Akwa Ibom.

Adel Amrouche tsohon mai horar da tawagar 'yan wasan Libya.
Adel Amrouche tsohon mai horar da tawagar 'yan wasan Libya. Duisaf.com
Talla

Amrouche ya shaidawa manema labarai cewa, ya yanke shawarar ajiye aikin horar da Libyan ne saboda ko kadan baya jin dadin irin yanayin tafiyar da ayyukan horar da ‘yan wasan kasar.

A watan Mayu da ya gabata, Libya ta dauki Amrouche mai shekaru 50, a mtsayin kocin ‘yan wasanta, wanda a makon da ya gabata, ya jagorancin wasan da Libyan ta tashi canjaras (0-0) tsakaninta da Afrika ta Kudu.

Baki dayan wasannin neman cancantar zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afrika da Libya ta buga da sunan a gida, ta fafata su a wasu kasashen na dabam, la’akari da matsalar rashin tsaron da ta addabi kasar.

Tuni dai hukumar kwallon kafar kasar ta Libya ta bayyana Omar Al-Marime a mtsayin sabon kocin da zai jagoranci ‘yan wasanta, wasan da zasu fafata da Najeriya a gobe Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.