rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Monaco ta sallami kocinta saboda rashin karsashi

media
Leonardo Jardim REUTERS/Eric Gaillard

Kungiyar Kwallon Kafa ta Monaco da ke Faransa ta kori kocinta, Leonardo Jardim sakamakon rashin karsashin da kungiyar ke fuskanta a wannan kakar.


Monaco ita ce ta uku a can kasan teburin gasar Lig 1, yayin da ake ganin Thierry Henry ne zai maye gurbin Jardim don ci gaba da horar da ‘yan wasan na Monaco.

Jardim ya taimaka wa Monaco lashe gasar Lig 1 a shekarar 2017, wanda shi ne karon farko tun shekarar 2000.

Kocin ya kuma taimaka wa kungiyar wajen kaiwa matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai ta shekarar 2016-2017.

Kazalika ya taimaka wa wajen gina ‘yan wasa irinsu Kylian Mbappe da yanzu haka ke taka leda a PSG.

A shekarar 2014 ne Monaco ta kulla kwantiragi da Jardim mai shekaru 44.