rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Pillars da Rangers za su fafata wasan karshe na gasar kofin Aiteo

media
Kofin gasar kalubale ta kungiyoyin Najeriya (Aiteo Cup) Photo credit: Aiteo cup

Kungiyoyin Enugu Rangers da Kano Pillars sun samu nasarar kaiwa zagayen karshe na gasar cin kofin kalubalen Najeriya wato Aiteo Cup.


A ranar Laraba ne dukkanin kungiyoyin biyu, suka fafata wasannin kusa dana karshe, inda a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano, Enugu Rangers suka samu nasara akan Nasarawa United da kwallaye 4-2.

Nasarawa United ce dai ta soma jefa kwallaye biyu a a wasan, kafin daga bisani Enugu Rangers sun rama, tare da kara kwallaye biyu.

Wasan tsakanin Kano Pillars da Katsina United kuwa ya gudana ne a birnin Legas, wanda aka tashi 2-2, hakan yasa aka kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Pillars ta samu nasara kan Katsina United da kwallaye 4-1.

A ranar 24 ga watan Oktoban da muke ciki, za’a buga wasan karshe na gasar cin kofin kalubalen na Aiteo a filin wasa na Stephen Keshi dake garin Asaba a jihar Delta.

Kungiyar da ta yi nasarar lashe kofin na Aiteo ce za ta wakilci Najeriya, a gasar cin kofin kalubale na zakarun kungiyoyin nahiyar Afrika a kaka mai zuwa, wato CAF Confederations Cup.