Isa ga babban shafi
Wasanni

Sporting Lisbon ta sallami dadadden Kocinta

Kungiyar kwallon kafa ta Sporting Lisbon ta sanar sallamar kociyanta Jose Peseiro yau Alhamis biyo bayan shan kaye a hannun Estoril FC da ci 2 da 1.Ka zalika rashin nasarar ta Lisbon a hannun Estoril ita ce irinta ta hudu a jere karkashin wasannin gasar League.

Ka zalika rashin nasarar ta Lisbon a hannun Estoril ita ce irinta ta hudu a jere karkashin wasannin gasar League.
Ka zalika rashin nasarar ta Lisbon a hannun Estoril ita ce irinta ta hudu a jere karkashin wasannin gasar League. REUTERS/Rafael Marchante
Talla

Sanarwar sallamar Peseiro wadda ke fitowa daga bakin shugaban Club din Frederico Varandas na zuwa ne duk da kasancewar Sporting a matsayin ta 5 kuma tazarar maki 2 kacal tsakaninta da FC Porto wadda ke saman teburi a gasar ta League.

Sallamar Peseiro mai shekaru 58 daga Sporting dai ya kawo karshen tsawon lokacin wa’adi biyu da ya shafe yana horar da kungiyar wadda ya kai ga wasan karshe na lashe kofin Europa a shekarar 2005.

Kazalika duk da gazawarta a gasar League Sporting za ta kai zagayen kungiyoyi 16 na gasar Europa inda ta ke matsayin ta biyu a rukunin da ta ke na E tazarar maki 2 tsakaninta da Arsenal da ke saman teburi kazalika ta dara FC Vorskla da maki 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.