rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Zakarun Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Manchester United ba ta cancanci nasara a wasanmu ba - Ronaldo

media
Ko a bara ma dai yayin gasar cin kofin zakarun Turai Juventus din sai da ta kai wasan gab dana karshe amma Madrid mai rike da kambun ta yi waje da ita. Marco BERTORELLO / AFP

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus Cristiano Ronaldo ya ce tsohuwar kungiyarsa Manchester United ba ta cancanci yin nasara a wasan da ya gudana tsakaninsu jiya laraba ba, wasan da Man U din ta lallasa Juventus da ci 2 da 1.


A cewar Ronaldo wanda ya zura kwallo a wasan na jiya cikin minti na 55 da fara wasa, Juventus ce ta yi rawar gani a wasan kuma babu shakka da sun samu cikakken dama da sa a da sun ragargaji United.

Wasan na jiya dai shi ne karon farko da Juventus ta sha kaye cikin wasanni 15 tun bayan sauya shekar Ronaldon zuwa gareta daga Real Madrid a watan Yulin da ya gabata kimanin watanni biyar kenan, haka zalika ita ke saman teburi a bangaren gasar Serie A, yayinda ta ke matsayin zakara a rukuninta na H a wasannin gasar cin kofin zakarun Turai.

A cewar Ronaldo dole ne ‘yan wasan na Juventus su zage damtse la’akar da muhimmancin gasar matukar dai suna bukatar dage kofin na zakarun Turai a wannan shekara.

Ko a bara ma dai yayin gasar cin kofin zakarun Turai Juventus din sai da ta kai wasan gab dana karshe amma Madrid mai rike da kambun ta yi waje da ita.