rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa CAF

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ahmed Musa ya shigar da karar alkalin wasa a CAF

media
Ahmed Musa REUTERS/Stefano Rellandini

Dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya bukaci Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika da ta gudanar da bincike domin tantance sahihancin kwallaye 2 da Super Eagels ta jefa a ragar Afrika ta Kudu amma alkalin wasa ya soke a karawar da suka yi a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika.


Alkalin wasan dan asalin Gambia, Bakary Gassama ya soke kwallayen da Kelechi Iheanacho da Ahmed Musa suka zura a ragar Afrika ta Kudu.

Koda yake alkalin ya amince da tafka kuskure , sannan kuma ya nemi afuwan Musa, in da yace, wani lokacin ana samun irin wannan kuskuren musamman saboda rashin na’urar taimaka wa alkalin wasa.

Tuni dai Najeriya ta samu nasarar samun tikitin halartar Gasar Cin Kofin Afrika a Kamaru a shekara mai zuwa duk da cewa ta tashi wasan ne 1-1 da Afrika ta Kudu a Johannesburg.