rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mata sun buga kwallon kafa a cikin zauren Majalisar Birtaniya

media
Wasu mata mambobin Majalisar Dokokin Birtaniya da suka taka leda a zauren Majalisar news.sky.com

An caccaki wasu mata mambobin Majalisar Dokokin Birtaniya saboda yadda suka buga kwallon kafa a cikin zauren Majalisar.


Daya daga cikin matan Hannah Bardell ta wallafa hotunansu a shafin sada zumunta da ke nuna yadda suke buga kwallon sama bayan an dage zaman Majalisar a yammacin ranar Talata.

Da farko dai an shirya cewa,  matan za su buga wani wasa a kungiyar kwallon kafa ta matan Majalisar Dokokin Birtaniya a ranar Talata, amma aka dage wasan bayan ya ci karo da wani zaman kada kuri’a a Majalisar Dokokin.

Sai dai bayan watsewar Majalisar, ‘yan matan sun sanya rigunan kwallon kafa tare da nuna dabarunsu na taka leda, kuma har suka yada wa duniya ta kafafen sada zumunta.

Mai magana da yawun Majalisar, John Bercow ya ce, bai kamata a rika amfani da zauren Majalisar mai cike da tarihi wajen gudanar da wasu ayyuka na daban ba.