rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Cin Kofin Afrika Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya za ta fafata da Kamaru a wasan kusa dana karshe

media
'Yan wasan Najeriya Super Falcons, yayin murnar lallasa Equatorial Guinea da kwallaye 6-0 a gasar cin kofin nahiyar Afrika ajin mata dake gudana a Ghana. (24/11/18). Premium Times Nigeria

Yau Talata tawagar ‘yan wasan Najeriya Super Falcons za su fafata wasan kusa dana karshe da Kamaru a gasar cin kofin nahiyar Afrika ajin mata.


Duk wanda ya samu nasarar kaiwa matakin wasan karshe, tsakanin Najeriya da Kamaru, to shi ne zai halarci gasar kwallon kafar cin kofin duniya ajin mata, da Faransa za ta karbi bakunci a shekarar 2019.

Da fari dai Najeriya mai rike da kofunan gasar nahiyar afirka ajin mata har guda takwas, ta soma gasar bana ce da kara hagu, inda Afrika ta kudu ta samu nasara kanta da kwallo 1-0.

Amma daga bisani a sauran wasanninta na rukuni, Najeriya ta lallasa Zambia da kwallye 4-0, sai kuma Equatorial Guinea da Najeriyar ta lallasa da kwallaye 6-0.