rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa Gasar Cin Kofin Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ian Wright ya yabawa Emery dangane da ajiye Ozil a benci

media
Mai horar da kungiyar Arsenal Unai Emery. REUTERS/David Klein

Tsohon dan wasan Arsenal Ian Wright ta yabawa kocin kungiyar Unai Emery, saboda rashin fargaba ko jin nauyin ajiye duk wani kwararren dan wasan kungiyar da himmarsa ta yi kasa.


Wright, ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci kan matakin Emery ya dauka na ajiye Ozil a benci yayin wasan ranar Lahadin nan da Arsenal ta samu nasara kan Bournemouth da kwallaye 2-1.

Mesut Ozil ne dan wasan dake kan gaba wajen albashi mai tsoka a Arsenal inda yake amshe Fam dubu 350,000 a kowane mako.

Matakin hutar da Ozil dai kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito na da nasaba da gazawarsa wajen taimakawa kungiyar yadda ya kamata a wasanni uku da suka buga jere da juna inda suka yi canjaras a dukkaninsu.