Isa ga babban shafi
Wasanni

CAF ta yiwa Afrika ta Kudu tayin karbar bakuncin gasar AFCON

Shugaban kwallon kafa na Afrika ta Kudu, Danny Jordaan ya ce, hukumar kula da kwallon nahiyar Afrika CAF, ta yi tayin basu damar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika a shekarar 2019 mai kamawa.

Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika Ahmad Ahmad.
Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika Ahmad Ahmad. CAF
Talla

CAF ta gabatarwa da Afrika ta Kudu tayin ne cikin gajeren wa’adi bayan daukar matakin kwace damar da ta baiwa Kamaru a karkashin shugabancin tsohon shugaban hukumar ta CAF Isa Hayatou.

A halin yanzu ana dakon shawarar da kasar zata yanke idan aka gana tsakanin gwamnatin Afrika ta Kudu da kuma hukumar kula da kwallon kafar kasar.

A cewar CAF, ta dauki matakin ne a dalilin rashin gamsuwa da shirin kasar Kamaru na kammala ayyukan karbar bakuncin gasar.

Za’a soma gasar kwallon kafar ta nahiyar Afrika daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga watan Yuli, bayan sauya lokacin gudanar da gasar na watannin Janairu da Fabarairu.

A karon farko dai kasashe 24 ne za su fafata a gasar mai zuwa, sabanin guda 16 da aka saba gani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.