rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tennis Australia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Serena Williams za ta shiga gasar Australian Open ta 2019

media
Serena Williams, shahararriyar 'yar kwallon tennis ta duniya. AFP

Masu shirya gasar kwallon tennis ta Australian Open sun bada tabbacin cewa Serena Williams za ta fafata wajen neman lashe kofin gasar da za’a watan Janairun sabuwar shekara.


Karo na farko kenan da Serena Williams za ta shiga gasar tun bayan wadda ta lashe kofinta a shekarar 2017, a lokacin da take dauke da juna biyu na watanni 8.

Haihuwar da Serena tayi a watan Satumba ne ya hana ta damar shiga gasar ta Australian Open a watan Janairun wannan shekara, sai dai ta fafata a gasannin Wimbledon da US Open har zuwa matakin wasannin karshe, inda ta sha kaye a dukkaninsu.

Har yanzu dai Serena Williams na da yawan kofuna 23 ne na manyan gasannin kwallon tennis da ta lashe a tsawon fafatawar da tayi a fagen wasan.