Isa ga babban shafi
Wasanni

Club 7 na neman gurbi 4 a zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai

Kungiyoyin kwallon kafar Turai 7 ciki har da Paris St Germain da Liverpool da kuma Inter Milan yanzu haka za su fafata don neman gurbi 4 da ya rage na kungiyoyi 16 da za su tafi zagaye na biyu na cin kofin zakarun Turai.

Cikin kungiyoyin 7 har da Liverpool da PSG da kuma Intermilan wadanda dukkaninsu ke faftukar ganin sun samu tsallakewa zuwa zagayen kungiyoyi 16 na gasar ta cin kofin zakarun Turai.
Cikin kungiyoyin 7 har da Liverpool da PSG da kuma Intermilan wadanda dukkaninsu ke faftukar ganin sun samu tsallakewa zuwa zagayen kungiyoyi 16 na gasar ta cin kofin zakarun Turai. REUTERS/Peter Nicholls
Talla

A rukunin C mai cike da sarkakiya, Liverpool da ke matsayin ta 3 da maki 6  za ta kara da Napoli jagora mai maki 9 yayinda ita kuma PSG da ke matsayin ta 2 da maki 8 za ta kara da Redstar mai maki 4.

A bangare guda ita kuma Inter Milan ta dogara ne da nasarar Barcelona kan Tottenham don itama ta samu wucewa zuwa zagayen kungiyoyin 16.

Matukar dai Liverpool na fatan zuwa zagayen gaba a gasar to dole ne ta yi gagarumar nasara kan Napoli jagora ba kuma tare da bari an zura mata kwallo ba, yayinda ita kuma Napoli za ta iya samun damar wucewa zagayen kungiyoyin 16 ko da kuwa PSG ta yi rashin nasara kan Redstar.

Matukar dai kungiyoyin 3 Napoli, PSG da kuma Liverpool suka kare wasan a maki 9-9 to fa za a duba yanayin nasarar kowanne bangare yayinda Club din da ba a taba nasara kansa ba zai zama a saman teburi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.